27يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا لا تَدخُلوا بُيوتًا غَيرَ بُيوتِكُم حَتّىٰ تَستَأنِسوا وَتُسَلِّموا عَلىٰ أَهلِها ۚ ذٰلِكُم خَيرٌ لَكُم لَعَلَّكُم تَذَكَّرونَAbubakar GumiYã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna.