Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu kanã sanin abin ƙyãma a cikin fuskõkin waɗanda suka kãfirta sunã kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karãtun ayõyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Yã yi alkawarinta ga waɗanda suka kãfirta. Kuma makõmarsu ta mũnana.