87قالوا ما أَخلَفنا مَوعِدَكَ بِمَلكِنا وَلٰكِنّا حُمِّلنا أَوزارًا مِن زينَةِ القَومِ فَقَذَفناها فَكَذٰلِكَ أَلقَى السّامِرِيُّAbubakar GumiSuka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa."