94قُل إِن كانَت لَكُمُ الدّارُ الآخِرَةُ عِندَ اللَّهِ خالِصَةً مِن دونِ النّاسِ فَتَمَنَّوُا المَوتَ إِن كُنتُم صادِقينَAbubakar GumiKa ce: "Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku, a wurin Allah keɓe bã da sauran mutãne ba, to, ku yi gũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya."