Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kãfirai.