Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba. Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi.