271إِن تُبدُوا الصَّدَقاتِ فَنِعِمّا هِيَ ۖ وَإِن تُخفوها وَتُؤتوهَا الفُقَراءَ فَهُوَ خَيرٌ لَكُم ۚ وَيُكَفِّرُ عَنكُم مِن سَيِّئَاتِكُم ۗ وَاللَّهُ بِما تَعمَلونَ خَبيرٌAbubakar GumiIdan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.