262الَّذينَ يُنفِقونَ أَموالَهُم في سَبيلِ اللَّهِ ثُمَّ لا يُتبِعونَ ما أَنفَقوا مَنًّا وَلا أَذًى ۙ لَهُم أَجرُهُم عِندَ رَبِّهِم وَلا خَوفٌ عَلَيهِم وَلا هُم يَحزَنونَAbubakar GumiWaɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma bã su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gõri, ko cũta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.