Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.