A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu. Ka ce: "Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun haɗa da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.