201وَمِنهُم مَن يَقولُ رَبَّنا آتِنا فِي الدُّنيا حَسَنَةً وَفِي الآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنا عَذابَ النّارِAbubakar GumiKuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!"