Kuma ku cika hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne.