Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku. Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.