Ku ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne."