132وَوَصّىٰ بِها إِبراهيمُ بَنيهِ وَيَعقوبُ يا بَنِيَّ إِنَّ اللَّهَ اصطَفىٰ لَكُمُ الدّينَ فَلا تَموتُنَّ إِلّا وَأَنتُم مُسلِمونَAbubakar GumiKuma lbrãhĩm ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙũbu (ya yi wasiyya, suka ce:) "Yã ɗiyãna! Lalle ne, Allah Ya zãɓã muku addini don haka kada ku mutu, lalle, fãce kuna Musulmi."