5وَلَقَد أَرسَلنا موسىٰ بِآياتِنا أَن أَخرِج قَومَكَ مِنَ الظُّلُماتِ إِلَى النّورِ وَذَكِّرهُم بِأَيّامِ اللَّهِ ۚ إِنَّ في ذٰلِكَ لَآياتٍ لِكُلِّ صَبّارٍ شَكورٍAbubakar GumiKuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa, "Ka fitar da mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan (masĩfun) Allah." Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai gõdiya.