18مَثَلُ الَّذينَ كَفَروا بِرَبِّهِم ۖ أَعمالُهُم كَرَمادٍ اشتَدَّت بِهِ الرّيحُ في يَومٍ عاصِفٍ ۖ لا يَقدِرونَ مِمّا كَسَبوا عَلىٰ شَيءٍ ۚ ذٰلِكَ هُوَ الضَّلالُ البَعيدُAbubakar GumiMisãlin waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da tõka wadda iska ta yi tsananin bugãwa da ita a cikin yini mai gũguwa. Ba su iya amfãni daga abin da suka yi tsirfa a kan kõme. Wancan ita ce ɓata mai nĩsa.