11قالَت لَهُم رُسُلُهُم إِن نَحنُ إِلّا بَشَرٌ مِثلُكُم وَلٰكِنَّ اللَّهَ يَمُنُّ عَلىٰ مَن يَشاءُ مِن عِبادِهِ ۖ وَما كانَ لَنا أَن نَأتِيَكُم بِسُلطانٍ إِلّا بِإِذنِ اللَّهِ ۚ وَعَلَى اللَّهِ فَليَتَوَكَّلِ المُؤمِنونَAbubakar GumiManzanninsu suka ce musu, "Bã mu zama ba fãce mutãne misã, linku, kuma amma Allah Yanã yin falala a kan wanda Yake so daga bãyinsa, kuma bã ya kasancẽwa a gare mu, mu zo muku da wani dalĩli fãce da iznin Allah. Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara.