Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ¦ayansu ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa."