102ذٰلِكَ مِن أَنباءِ الغَيبِ نوحيهِ إِلَيكَ ۖ وَما كُنتَ لَدَيهِم إِذ أَجمَعوا أَمرَهُم وَهُم يَمكُرونَAbubakar GumiWannan daga lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.