36وَأوحِيَ إِلىٰ نوحٍ أَنَّهُ لَن يُؤمِنَ مِن قَومِكَ إِلّا مَن قَد آمَنَ فَلا تَبتَئِس بِما كانوا يَفعَلونَAbubakar GumiKuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa.