18وَمَن أَظلَمُ مِمَّنِ افتَرىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا ۚ أُولٰئِكَ يُعرَضونَ عَلىٰ رَبِّهِم وَيَقولُ الأَشهادُ هٰؤُلاءِ الَّذينَ كَذَبوا عَلىٰ رَبِّهِم ۚ أَلا لَعنَةُ اللَّهِ عَلَى الظّالِمينَAbubakar GumiKuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan anã gitta su ga Ubangijinsu, kuma mãsu shaida su ce: "Waɗannan ne suka yi ƙarya ga Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."