110وَلَقَد آتَينا موسَى الكِتابَ فَاختُلِفَ فيهِ ۚ وَلَولا كَلِمَةٌ سَبَقَت مِن رَبِّكَ لَقُضِيَ بَينَهُم ۚ وَإِنَّهُم لَفي شَكٍّ مِنهُ مُريبٍAbubakar GumiKuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.