Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna.